AdSense

Na Sayar Da Gashi Na Dala Biyu Domin Na Saya Wa Yara Na Abinci


Ranar da Prema Selvan ta sayar da gashin kanta a kan kudi dala biyu domin ta saya wa 'ya'yanta abinci ita ce rana mafi muni a rayuwarta.

Prema ta kasance tana da 'ya'ya uku, kuma ba ta da miji saboda ya kashe kansa ne sakamakon tsananin damuwar da ya tsinci kansa a ciki baya ga dumbin bashin da ake binsa, sannan kuma duk wani tunani na jin dadin duniya da yake bai samu ba.

Ita kuwa duk da haka tana da fatan cewa wata rana za ta ji dadi.

To amma bayan da ta sayar da gashin kanta, sai abubuwa suka fara sauya mata.

Kafin mutuwar mijinta, Prema da mijin nata na aiki ne a wani wajen da ake yin bulo a jihar Tamil Nadu da ke kudancin Indiya, inda dukkansu suke samun abin da zai ishe su tare da iyalansu.

To amma duk da haka suna fatan samun karin a kan abin da suke samu.

Mijin nata ya dauki bashi domin ya fara nasa buga bulon, to amma sai aka yi rashin sa'a abin bai yi wu ba, hakan ya sa saboda tsananin damuwar da ya shiga, sai ya kashe kansa a shekarar da ta gabata.

Daga nan sai Prema ta shiga matsin rayuwa, kudin ciyar da 'ya'yanta da kayan da za su saka kai yadda za ta biya bashin da mijinta ya karbo ma ya gagara.

To amma duk da haka ta rinka yin kokari tana zuwa wajen aikinta inda ake yin bulo tare da 'ya'yanta kananan biyu.

Prema ta shaida wa BBC cewa, ' A kullum idan naje aiki ina samun rupee 200, kwatankwacin dala kusan uku, kuma ya kan isheni mu ci mu sha ni da 'ya'yana'.

Katsam sai Prema ta fara rashin lafiya, abinda ya rinka hanata zuwa wajen aiki.

Ta ce 'Bana iya daukar abu mai nauyi, ina zama a gida kusan ko da wanne lokaci saboda tsananin zafin zazzabi.
Prema ta shafe watanni uku ta na jinya, sai da ta kai ba bu komai a gidanta komai ya kare.

Ta ce ' Wata rana ina zaune sai babban da na dan shekara bakwai ya dawo daga makaranta ya ce mini ya na jin yunwa, na yi shiru daga nan sai ya fara kuka saboda yunwa''

' Bani da ko kwandala, haka bani da abinda zan sayar mu ci abinci, daga nan ne sai na yi tunanin cewa ina da abin sayarwa'. Inji Prema.

Ta ce ' Na tuna wajen da ake siyan gashi, daga nan sai na yi maza na je na aske gashin kai na na sayar a kan dala biyu.

India dai na daya daga cikin kasashen da suke fitar da gashin kai wanda ake sayarwa a sassan duniya.

Akwai wasu masu bauta a kasar wanda suka yi imanin cewa idan har suka sadaukar da gashin kansu, to addu'arsu na karbuwa.
Ba wai Prema ta samu wani makudan kudi ba ne, ta dai samu dan abin da za su sayi abinci mai dan dama.

Daga na Prema ta fara tunanin cewa idan har abincin da ta saya ya kare dole ta shiga damuwa, nan ta fara sake-sake inda za ta rayu tare da 'ya'yanta.

Ta je wani shago inda ta yi tunanin ta samu wani abu a wajen domin ta kashe kanta da shi.

To amma ganin irin halin da take ciki, sai mai shagon ya ki sayar mata komai, sai ta koma gida inda ta fara tunanin hanyar da za ta kashe kanta, can sai ga 'yar uwarta wadda ta kai mata ziyara sai ta hana ta.

Bayan wasu 'yan kwanaki, taimakon da ta jima tana nema sai kawai ta samu.
Bala Murugan ya samu labarin halin da Prema take ciki daga wajen wani abokinsa wanda ke da gidan bulo, daga nan sai ya tuna baya lokacin da shi ma da iyalansa suka shiga tsananin talauci.

Bala ya san irin yanayin da wanda talauci ya masa katutu ke tsaintar kansa, a lokacin da yake shekara 10 a duniya, sun fuskanci matsala ta rashi dan akwai lokacin da ko kwayar abinci babu a gidansu sai mahaifiyarsa ta sayar da tsoffin litattafansu da jaridun da suka tara ta sai musu shinkafa.

Bayan da abincin ya kare, sai mahaifiyar ta fara tunanin kashe kanta da kuma 'ya'yanta, daga baya sai ta fasa, sai wasu 'yan uwanta suka kai ta asibiti.

Yanzu Bala ya girma bayan ya sha gwagwarmaya, a yanzu yana da wajen zane-zane da aiki da komfuta na kansa.
Yanzu Bala na da damar taimakawa irin mutanen da ke matukar bukatar taimako.

Bala ya shaida wa Prema irin gwagwarmayar da ya sha, shi da wani abokinsa sun ba wa Prema kudi domin ta sayi wasu kayan abinci.

Daga nan sai Bala ya wallafa labarin Prema a kafafan sada zumunta, a cikin kwana daya tal sai da aka tarawa Prema dala 1,600.

Bala ya ce 'A lokacin da na shaida wa Prema cewa ga irin kudin da aka tara mata, sai ta yi murna sosai, har ta ce ya ishe ta ta biya wasu daga cikin bashin da ake binta'.

Prema ta ce tara mata kudin da ake ya isa haka, domin za ta koma bakin aikinta sai ta biya sauran bashinta a hankali.

Yanzu haka akwai sauran bashin da ake bin ta da ya kai dala 10, kuma mahunkunta a garin da suke sun shiga cikin al'amarinta inda suka yi mata alkawarin cewa za su taimaka mata ta zama dila ta sayar da madara a garinsu.

A hankali-a hankali, yanzu Prema ta fara tsayawa da kafafunta, to amma abin takaicin shi ne akwai miliyoyin Indiyawa da suke cikin halin matsi irin Prema duk kuwa da cigaban da tattalin arzikin kasarsu ke samu.

A cewar bankin duniya, Indiya ita ce kasa ta biyu ta al'ummarta ke fama da matsanancin talauci.
Duk da ya ke Prema ba ta iya karatu da rubutu ba, yanzu ta gane cewa akwai tsare-tsaren gwamnatin kasarsu da suke taimaka wa talakawa kamar ita.

Ta ce babu abinda za ta cewa gwamnatin jiharsu ta al'ummar wajen da ta ke zaune da kuma uwa uba Bala, wanda ya yi alkawarin cewa zai ci gaba da taimaka mata har yaranta su girma su yi karatu suma su taimaka mata.

Prema ta ce 'Yanzu na gane cewa mutum ya kashe kansa saboda matsala, ba mataki ne mai kyau ba.

No comments

Powered by Blogger.